Wata gobara ta lalata shaguna da dama a babbar kasuwar Gusau da ke jihar Zamfara inda kuma ta kashe mutum daya.
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9, na daren ranar Litinin a bangaren kayan ɗaki na babbar kasuwar.
Karanta wannan: Mutane 50 sun mutu bayan nutsewar kwale-kwalensu a Congo
Kwamandan hukumar kashe gobara na kasa, Hamza Mohammed, ya sanar da gidan talabijin na Channels cewa wani mai shago wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya mutu a lokacin da yake kokarin shiga shagonsa domin kashe gobarar.
Jami’an kashe gobara daga rundunar ‘yan sandan jihar sun yi ta fama da gobarar tun karfe 9 na dare domin hana yaduwar ta zuwa wasu shaguna.