Mutum 91 aka kashe a rikicin Mangu – Shugaban Matasa

Rikicin, barke, Plateau, kashe, mangu
Shugaban Kungiyar Matasan Mwaghavul na Kasa, Kwamared Sunday Dankaka, ya ce mutane 91 aka kashe, sannan aka jikkata wasu 158 a rikicin da ya barke a Karamar...

Shugaban Kungiyar Matasan Mwaghavul na Kasa, Kwamared Sunday Dankaka, ya ce mutane 91 aka kashe, sannan aka jikkata wasu 158 a rikicin da ya barke a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato a makon jiya.

Sunday Dankaka ya shaida wa manema labarai a Jos a ranar Talata cewa wadanda aka kashe sun hada da mata 42, yara 37 da maza 12 sannan aka kona gidaje 114 da masallatai 9 da coci 15.

Darakta na kungiyar Equity International Initiative, Chris Iyama, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen tallafa wa al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari a kananan hukumomin Mangu da Bokkos na jihar.

Karanta wannan: Gobara ta lalata dukiya mai yawa a babbar kasuwar Gusau

“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta kwato su tare da tabbatar da duk filayen noma da gidajen da masu su suka tsere suka bari, domin duk manoman da suka bar filayen kakanninsu su samu kwanciyar hankali su koma yankunansu da gonakinsu.

“Muna kuma kira ga Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Kasa da ta kara kaimi wajen bayar da agaji ga daukacin al’ummomin da abin ya shafa,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here