Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya mayarwa babban mai hamayya da shi na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar martani bayan sukar gwamnatinsa.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jami’iyyar hamayya ta PDP a zaben da ya gabata, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya sauka daga shugabancin kasar idan ba zai iya shawo kan matsalolin tsaron da kasar ke fama da su ba.
Karanta wannan: Mutum 91 aka kashe a rikicin Mangu – Shugaban Matasa
Atiku Abubakar, wanda shugaba Tinubu ya kayar a zaben da ya gabata, ya zargi shugaban da yin wasa da aikinsa yayin da kasar ke nutsewa cikin matsalar tsaro da ta tabarbarewar tattalin arziki.
Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta yi watsi da kalaman na Atiku tana mai cewa wata suka ce irin ta ‘yan hamayya.
A sanarwar martani da ta fitar, fadar shugaba Bola Tinubu ta ce har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku.
Karanta wannan: Gobara ta lalata dukiya mai yawa a babbar kasuwar Gusau
“Mun san cewa har yanzu zafin shan kaye bai saki Atiku ba don haka zai iya furta komai na sukar shugaba Tinubu,” in ji sanarwar.
Idan ba’a manta ba, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu kan yadda yake tafiye-tafiye a daidai lokacin da Najeriya ke dabaibaye da kalubalen tsaro.
Karanta wannan: Gwamna Adeleke ya sanya dokar hana fita bayan mutuwar mutum 2 a rikicin Jihar Osun
Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023 da ta gabata, ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ce masu garkuwa da mutane na cin karensu babu babbaka a kasar.
A kullum dai gwamnatin shugaba Bola Tinubu na bada bayyanan ƙoƙarin da take na shawo kan matsalar tsaro da tattalin arziƙi da sauran matsalolin da Najeriya ke fama da su, sai dai kuma ana ganin matsalolin na ci gaba da ƙaruwa ne.