Abuja: ‘Yan Bindiga sun bukaci tallafin kayan abinci da Naira Miliyan 290

'Yan bindiga, Kujuru, mata, sace, hari
‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari garin Banono da ke karkashin masarautar Kufana ta karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya,..

Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da mazauna Kuduru mutum 7 makwabciyar karamar hukumar Bwari a Abuja sun bukaci a biya su Naira miliyan 290 domin su sako mutanen da suka yi garkuwa da su.

Mazauna yankin da suka hada da mace mai juna biyu da yara uku da manya hudu wadanda suka shafe wata daya da kwana hudu a hannun ‘yan fashin sun yi awon gaba da su ne a ranar 28 ga watan Janairu.

A cewar wani shugaban al’ummar da ya bukaci a sakaya sunansa, ‘yan bindigar sun yi barazanar kashe biyu daga cikin wadanda abin ya shafa matukar ba’a biya Naira miliyan 290 a kan lokaci ba.

Karanta wannan: Har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku – Tinubu

Ya ce masu garkuwan sun kuma bukaci kayayyakin abinci da magunguna da zanin gado da sauransu.

“Sun tuntube mu mu kawo Naira miliyan 290 domin a sako su ko kuma su kashe biyu daga cikinsu. Muna da mace mai ciki da ’ya’ya uku a cikinsu,” inji shi.

“Sun ce mu kawo buhunan shinkafa da fakitin Indomie da maganin tari da maganin rigakafi da zanin gado da da sauran abubuwa makamantansu.

Sun dage cewa dole sai an biya kudin fansa Naira miliyan 290 sannan su sako mutanenmu.”

Karanta wannan: Mutum 91 aka kashe a rikicin Mangu – Shugaban Matasa

Ya roki Kayode Egbetokun da Sufeto-Janar na ‘yan sanda da Taoreed Lagbaja da babban hafsan soji da su kawo daukin wadanda aka yi garkuwa da su.

“Mun san cewa suna iya bakin kokarinsu amma muna rokonsu da su ceto iyalanmu kamar yadda suka yi wa ‘yan uwa mata shida da Ariyos,” in ji shi.

“Mun fahimci cewa mutanen sun riga sun kamu da rashin lafiya a zaman talala saboda tsananin yanayi da kuma jinyar da ake yi a wurin.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here