Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Kabir Yusuf, ya amince da raba kyautar kudi Naira dubu 20 don yin shagalin Babbar Sallah ga ma’aikatan gwamnati a fadin jihar da kananan hukumomi 44.
A cewar wata sanarwa da sakataren yada labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Musa Tanko Muhammad, ya fitar ranar Litinin, ya ce an yi niyya yin wannan kyautar ne don tallafawa ma’aikata gabanin bikin Babbar Sallah mai zuwa.
Sanarwar ta ce wadanda za au amfanar sune ma’aikatan gwamnati masu mataki na 01 zuwa 14 a ma’aikatun jihar da kuma ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar.
Ta bayyana cewa taimakon ya zo ne jim kafan bayan biyan albashin watan Mayu 2026, kuma yana nuna kudurin gwamnati na kula da jin dadin ma’aikata a Jihar Kano.
A cewar sanarwar, gwamnan ya ga dacewar a samar da karin sauki ganin halin tattalin arzikin da ake ciki da kuma bukatun kudi da ke tattare da lokutan bukukuwa.
“An yi niyyar wannan shiri ne don ba wa ma’aikata damar yin Sallah cikin farin ciki, kwanciyar hankali da iyalansu da kaunatattunsu,” in ji sanarwar.
Gwamnati ta kara da cewa wannan matakin ya kara nuna falsafar mulki na hada kowa da kowa da kuma kudirin tabbatar da cewa ma’aikata sun amfana daga manufofi da shirye-shiryen da suka fi amfanin jama’a.
Gwamna Yusuf ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na inganta jin dadin ma’aikata, habaka aiki a Kano.
Ya kuma mika gaisuwar Babbar Sallah ga ma’aikatan gwamnati da mazauna jihar, yana mai addu’ar zaman lafiya, hafin kai, da ci gaba da samun albarka ga Jihar Kano da Najeriya baki daya.












































