Kano: Fusatattun matasa sun kona ginin sakatariyar karamar hukuma kan karuwar rashin tsaro

Kano Map

Wasu fusatattun matasa da ke zanga-zangar kan karuwar rashin tsaro a ranar Lahadi sun kona wani bangare na ginin sakatariyar karamar hukumar Gwarzo a Jihar Kano.

Zanga-zangar da ta fara a matsayin ta lumana, saboda karuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankin, wanda mazauna ke cewa ya sa al’umma cikin tsoro da takaici.

Shaidun gani da ido sun ce daruruwan matasa sun fito kan tituna da tsakar rana, suna rera taken zanga-zanga da neman gwamnati ta dauki mataki na gaggawa don magance matsalar tsaro da ke kara tsananta.

An ruwaito cewa masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa Sakateriyar Karamar Hukuma, inda lamarin ya baci bayan wasu daga cikin matasan sun tilasta shiga ciki.

Cikin dan lokaci, aka fara kona wani bangare na ginin, yayin da hayaki wutar ya turnuke sararin sama lamarin da ya sa mazauna kusa da sakatariyar yin kaura cikin fargaba.

Wani mazaunin da ya shaida lamarin ya ce fushin ya na taruwa ne tsawon makonni. “Mutane sun gaji da kwana cikin tsoro, hare-haren sun yi yawa, kuma babu wani mataki da ake dauka, shi ya sa matasan suka yi haka,” in ji shi.

Wani mazaunin al’umma kuma ya roki a kwantar da hankali, yana gargadin cewa lalata kadarorin gwamnati na iya kara tsananta lamarin.

“Mun fahimci takaicin, amma tashin hankali ba zai magance matsalar ba. Abin da muke bukata shi ne tattaunawa da matakin tsaro na gaggawa,” in ji shi.

Daga baya jami’an tsaro sun tura runduna fadin karamar hukumar ta Gwarzo don dawo da doka da hana karin barna, yayin da hukumomi suka ce sun shiga tsakani don shawo kan rikicin da kuma binciken lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here