Buhari ya nada sabon shugaban gidan talabijin na NTA

Buhari signs signs 1
Buhari signs signs 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Salihu Dembos a matsayin sabon shugaban gida talabijin na NTA.

Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya fitar yau Laraba a Abuja.

Sanarwar ta ce sabon shugaban zai yi aiki na tsawon shekaru uku ne a ofishin.

“Kafin nadin nasa, Mista Dembos ya kasance a matsayin shugaban sashin kasuwanci na gidan talabijin din NTA.” Inji sanawarwar.

“Mista Dembos ya shafe sama da shekaru 20 a matsayin gogaggen dan jarida.”

Sanarwar ta kara da cewa Dembos ya rike matsayin shugaban talabijin din ta NTA a Lokoja da kuma Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here