Hukumar kididdiga ta jihar Kano ta sanar da shirin gudanar da cikakkiyar ƙidayar kan dukkan cibiyoyin karatun gaba da sakandare da ke fadin jihar, domin tattara sahihin bayanai kan fannin ilimi a matakin gaba da sakandare, wanda za a fara daga ranar Laraba 14 zuwa Juma’a 23 ga watan Janairun 2026.
Hukumar ta bayyana cewa aikin ƙidayar na tsawon kwanaki 10 zai shafi tattara bayanai kan adadi da nau’o’in cibiyoyin karatun gaba da sakandare da ke aiki a jihar Kano, yawan dalibai da shirye-shiryen karatu, kayayyakin more rayuwa kamar dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje da dakunan karatu na musamman, matsayin ma’aikata da ƙwarewarsu, da kuma halin da cibiyoyin ke ciki a yanzu.
Ta ce an tsara wannan ƙidaya ne domin samar wa masu tsara manufofi, cibiyoyin ilimi da sauran masu ruwa da tsaki bayanai sahihai da na zamani, domin inganta tsare-tsare, rarraba albarkatu yadda ya dace, da kuma habaka sakamakon ilimi a jihar.
Hukumar a wata sanarwa da ta fitar, ta yi kira ga dukkan cibiyoyin karatun gaba da sakandare da su ba da cikakken hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai ga jami’an kidaya da masu sa ido da za a tura domin gudanar da aikin.
Ta jaddada cewa nasarar ƙidayar ta ta’allaka ne da yadda cibiyoyin za su nuna gaskiya da gaggawa wajen amsa tambayoyi, tana mai bayyana cewa bayanan da za a tattara za su taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawara bisa hujjoji a fannin ilimi.
Domin karin bayani, hukumar kididdiga ta jihar Kano ta shawarci cibiyoyin ilimi da al’ummar jama’a da su tuntubi babban jami’in kididdiga na jihar Kano, Dakta Suraj Sulaiman, ta lambar waya 07032154410, ko kuma daraktan ayyukan Auwal Yau Muhammad, ta lambar waya 08069090468
Hukumar ta kuma bayyana cewa wannan ƙidaya na daga cikin manyan kokarin tattara bayanai da aka taba yi a bangaren ilimin gaba da sakandare a jihar Kano, wanda zai taimaka wajen fayyace karfi, gibin da kuma kalubalen da ke cikin tsarin ilimin a halin yanzu.













































