Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Emeka Nwite, ya mayar da kundin shari’ar kwamishinan kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, ga babban alkali domin sake ware wa wani alkalin, dangane da zargin tallafawa ayyukan ta’addanci da Dala Miliyan 9.7.
Alkalin ya yanke wannan hukunci ne bayan kotu ta koma aiki daga hutun shari’a, inda ya umarci a mayar da kundin shari’ar zuwa sashen rajista domin babban alkali ya sake ba da ita ga wani alkalin da zai ci gaba da sauraron karar.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa Yakubu Adamu, wanda tsohon manajan reshen Polaris Bank ne a Jihar Bauchi, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta tattalin arziki EFCC ke tuhumarsa da laifukan tallafawa ayyukan ta’addanci da wanke kuɗi.
Ana tuhumar kwamishinan tare da wasu mutum uku a kan tuhume-tuhume goma, inda sauran waɗanda ake tuhuma suka haɗa da Balarabe Abdullahi Ilelah, Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed, waɗanda dukkansu ma’aikatan gwamnatin Jihar Bauchi ne.
An gurfanar da waɗanda ake tuhuma gaban kotu, inda suka musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka karanta musu, yayin da alkalin ya ƙi amincewa da neman beli da suka gabatar, bisa hujjar cewa laifukan da ake tuhumarsu da su na barazana ga tsaron ƙasa da lafiyar jama’a.
Kotun ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Kuje tare da sanya ranar fara shari’a, tare da umarnin a saurari karar cikin gaggawa.
Sai dai a ranar da aka koma sauraron shari’ar, babu wani lauya da ya wakilci EFCC a gaban kotu.
Bayan jin bayanin lauyan waɗanda ake tuhuma, kotun ta lura da cewa shari’ar ta kasance cikin shari’o’in hutun kotu, sannan ta bayar da umarnin a mayar da kundin shari’ar domin babban alkali ya sake ware ta.
EFCC ta zargi waɗanda ake tuhuma da haɗa baki wajen bayar da kuɗi sama da Dala Miliyan Biyu domin tallafa wa Bello Bodejo da wasu da ke da alaƙa da shi, lamarin da ake zargin an yi shi ne da amincewar gwamnan Jihar Bauchi, inda ake cewa kuɗaɗen sun taimaka wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.













































