An kama jami’in DSS bisa zargin fyade da tilastawa yarinya Musulma sauya addini zuwa Kiristanci

Department of State Service DSS

Hukumar tsaron farin kaya DSS ta tabbatar da cafke ɗaya daga cikin jami’anta mai aiki, Ifeanyi Onyewuenyi, bisa wani mummunan ƙorafi na ke zargin sacewa, cin zarafin jima’i da kuma tilasta wa wata yarinya Musulma ’yar shekara 16 sauya addini zuwa Kiristanci.

An kai ƙorafin ne ta hanyar wata takardar koke da ofishin lauyoyi na Gamji Lawchain da ke Abuja, wadda aka miƙa wa babban daraktan DSS a madadin mahaifin yarinyar, Alhaji Abdulhadi Ibrahim.

Ƙorafin ya bayyana cewa an shafe kusan shekaru biyu ana fama da wannan lamari tun lokacin da aka sace yarinyar daga gidansu da ke yankin Hadejia a Jihar Jigawa, tana ƙarama.

Iyalin sun bayyana cewa sun shafe fiye da shekaru biyu suna neman Walida Abdulhadi ba tare da nasara ba, lamarin da ya jefa su cikin tsananin tashin hankali da damuwa.

Lauyoyin sun ƙara da cewa mahaifiyar yarinyar ta rasu sakamakon mummunan raɗaɗin zuciya da damuwar da ta shiga bayan ɓacewar ’yarta.

Karin labari: Gwamnatin Kano ta ba da umarnin yin bincike kan mutuwar matar aure sakamakon zargin sakacin likitoci a Asibiti

Bincike ya nuna cewa an samu ci gaba a lamarin ne lokacin da ake zargin jami’in DSS ya kira mahaifin yarinyar, inda ya bayyana cewa Walida tana tare da shi tsawon lokacin da ta ɓace, har ta haifi jariri a gare shi, sannan ya nuna aniyarsa na aure ta.

Bayan da wani wakilin iyalin ya je wata cibiyar DSS a Abuja domin bincike, an gano cewa ana zargin yarinyar ta zauna a cikin gidan DSS tsawon lokacin da ta ɓace.

Takardar koken ta jero manyan zarge-zarge da suka haɗa da cin zarafin jima’i ga yarinya wadda ba ta kai shekarun yarda ba, tilasta mata sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci ba tare da izinin iyayenta ba, da kuma amfani da wurin gwamnati mai tsaro wajen ɓoye ta daga iyalinta.

Lauyoyin iyalin sun buƙaci dakatar da jami’in nan take tare da gurfanar da shi gaban kotu, da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa kan cibiyar DSS ta Karmajiji, tare da tabbatar da sakin Walida da jaririnta cikin tsaro.

A wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a da sadarwa ta DSS, Favour Dozie, ya fitar, hukumar ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Sanarwar ta bayyana cewa DSS ba ta amince da irin wannan ɗabi’a ba, kuma idan bincike ya tabbatar da laifin, za a ɗauki matakan da suka dace bisa ƙa’ida, tare da alkawarin bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here