Kotu ta ci gaba da tsare Portable a gidan yarin Kwara bisa rashin cika sharuddan beli

Portable prison 750x430

Mawakin Najeriyar nan Okikiola Badmus, wanda aka fi sani da Portable, an tsare shi a gidan gyaran hali na Oke Kura da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara, bisa rashin cika sharuddan belin da wata kotun karamar hukuma ta gindaya a jihar.

Hakan ya biyo bayan bayyanar mawakin ne a gaban kotu a ranar Litinin kan zargin bata masa suna da fitaccen mawakin Fuji Akorede Saheed, A.K.A Saheed Osupa ya yi masa.

Sai dai mawakin ya samu beli a kan Naira miliyan 1 da wasu sharudda masu tsauri, ciki har da bayar da wadanda za su tsaya masa guda biyu.

A cewar umarnin kotun, daya daga cikin wadanda za su tsaya masa dole ne ko dai ya kasance shugaba ko sakataren kungiyar mawaka ta Najeriya, yayin da dayan kuma ya kasance mai mallakar kadarori a wani yanki da aka kebe na gwamnati a Ilorin, wanda ya samu takardar shaidar zama.

Karin bayani…..

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here