Sarkin Musulmi ya umarci Musulmi su fara duban jinjirin watan Muharram

Sultan of Sokoto Muhammad Saad Abubakar III 666x430

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya umarci Musulmin Najeriya da su shiga fara neman jinjirin watan Muharram 1448AH, wani aiki mai muhimmanci da zai tantance farkon Sabuwar Shekarar Musulunci.

Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban Kwamitin Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Sarkin Musulmi dake Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar.

Sanarwar ta ce ranar Litinin, 15 ga Yuni, 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Zulhijjah 1447AH, an ware ta domin duba jinjirin watan Muharram a fadin kasar, wato wata na farko a kalandar Musulunci.

Sarkin Musulmi ya roki Musulmi a fadin ƙasar da su kula sosai da sararin sama bayan faduwar rana, sannan su ba da rahoton duk wani ingantaccen labarin ganin jinjirin wata ta hanyoyin gargajiya da aka kafa.

A cewar sa, duk wani ingantaccen ganin wata da aka tabbatar ya kamata a isar da shi ga Hakimin Gari ko Shugaban Kauye mafi kusa domin ya isar da shi zuwa Majalisar Sarkin Musulmi zuwa ga Sarkin Musulmi.

“Wannan aikin duba jinjirin wata na shekara-shekara shi ne tushen tantance farkon wata sabuwar shekarar Musulunci, kuma wajibi ne na addini da al’ummar Musulmi ke yi a fadin Najeriya da ma duniya baki daya.

“Watan Muharram yana da muhimmanci musamman a Musulunci domin yana cikin watanni 4 mafiya tsarki, kuma shi ne farkon kalandar Musulunci wadda ke kayyade manyan bukukuwa da ibadoji na addini,” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here