Daga: Aminu bala madobi
Rahotanni sun nuna cewa a tsakar daren karshen makon nan ne wasu fusatattun matasa sukai dirar mikiya kan ƴan fashin wayar salula a unguwar Kabuga dake karamar hukumar Gwale a birnin Kano, inda suka ƙone Baburin adaidaita sahun ɗaya daga cikin yan Fashin waya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, ƴan fashin wayar sun yi yunƙurin aikata fashin, inda matasan da za a yi wa fashin wayar suka nemi taimakon jama’ar da ke kusa da wajen, kuma aka far musu.
Sai dai waɗanda ake zargin fashin wayar sun ranta a na kare a lokacin da akayi kokarin kama su , kuma suka bar baburin adaidaita sahun da suke aikata laifin fashin wayoyin ga jama’ar gurin.
Ganau din ya bayyana cewar jama’ar da ke wajen nan take sun bankawa Baburin adaidaita sahun wuta suka kone shi ƙurmus.
Domin samun shirye shiryen mu, latsa wannan alama????????
https://chat.whatsapp.com/HQU1Jxlop03HaIwUpwXc5A













































