Rahotanni sun ce an haifi wata jariri mai fuska biyu a wani kauye da ke arewacin Indiya, inda mahaifiyar ayanzu ke cigaba da murmurewa bayan haihuwar.
Jaririyar mai suna Lali, da alama tana da wani yanayi da ba kasafai ake samu ba da ake kira craniofacial duplication, inda kai ɗaya ke da fuska biyu hade da kwakwalwa.
Sai dai duk yanayin fuskar Lali sun ninnin ka – inda take da hanci biyu, leɓe biyu, da idanu biyu.
“‘yata tana da lafiya – kamar kowane yaro,” in ji Vinod Singh, mahaifin yarinyar da ya kasance ma’aikacin gona.
Kimanin mutane 100 ne ke ziyartar Lali a gidansu kowacce rana don taɓa kafafunta saboda girmamawa, suna ba da kuɗi da kuma samun albarka, in ji Singh ga Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.
Yarinyar ta samu karɓuwa cikin sauƙi a wajen manyan dangin Kumar, waɗanda suka ce ba su da shirin tuntubar likitoci don duba ko za a iya yiwa yarinyar tiyata ko gyara.
“Likitan ya ce komai daidai ne lokacin da aka haife ta. To ina bukatar samun taimakon likita?” Inji mahaifin yarinyar.
“Tana ci ta bakin ɗaya tana tsotsar babban yatsanta da ɗaya. Muna amfani da kowane bakin da ke da ‘yanci don ciyar da ita, “Kumar mai shekaru 24 ta shaida wa AFP, ta ƙara da cewa tana ci tana shaka a kullum.
Likitoci sun ce lamarin wani lamari ne da ba kasafai ake samun sa ba, inda yarinyar ke da kwarangwal guda biyu a hade wuri guda, kuma raba su ba abu ne mai wahala.
Sai dai likitocin sun ce kamata ya yi a binciki yarinyar sosai don yin nazari kan yiwuwar kamuwa da cuta.
“A bayyane yake yarinyar ba ta cikin haɗari amma dole ne a bincika ko kogon baki da na hanci da sauran wurare” suna aiki daidai, in ji likitan yara Gupta.












































