Kotun koli a jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan bangarorin da ke cikin shari’ar rikicin makarantar Prime College da gwamnatin jihar Kano da su ci gaba da kasancewa a yadda suke, har zuwa ci gaban sauraron karar.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Abdu Maiwada Abubakar na Kotun Koli mai lamba 17 da ke titin Miller Road, ya yanke wannan hukunci a ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025, bisa roƙon da lauyoyin Prime College suka gabatar.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa karar, wadda aka shigar da ita a ƙarƙashin lamba K/831/2025, ta hada da gwamnan Kano, Lauyan gwamnati, kakakin majalisar Dokoki ta jiha, jukumar kula da Makarantun masu zaman kansu da na sa-kai (KPVIB), da kuma sakataren hukumar, Comrade Baba Abubakar Umar, a matsayin wadanda ake tuhuma.
Karin labari: Gwamnatin Kano ta aika ƙorafe-ƙorafe kan Sheikh Lawan Triumph zuwa Majalisar Shura
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan gabatar da bukatar gaggawa da aka shigar ranar 22 ga Satumba, 2025, wacce ta samu goyon bayan rantsuwar shafi 43 da Mallam Musbahu Mohammed, jami’in hulda da jama’a na Prime College, ya yi.
A baya, wata kotun majistare da ke Gyadi-Gyadi ta soke umarnin da ta bayar na rufe makarantar, inda alƙaliyar kotun, Fauziyya Sheshe, ta bayar da umarnin a buɗe ta nan take.
Sai dai a ranar 16 ga Satumba, hukumar KPVIB ta shigar da ƙara a gaban kotun majistare inda aka bayar da umarnin ɗagewar aiki har zuwa lokacin da za a saurari karar a fili.
A wannan sabon hukunci, Mai shari’a Abubakar ya umurci bangarorin da su kiyaye matsayin da ake ciki yanzu har sai an kammala sauraron bukatar da aka shigar, tare da sanya ranar 7 ga Oktoba, 2025 domin sauraron karar a hukumance.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rashin jituwa tsakanin makarantu masu zaman kansu da hukumomin jihar kan batun kulawa da tsarin gudanarwa, lamarin da ya sa Prime College ke neman tsari ta hanyar kotu domin kare ayyukanta.













































