Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ibrahim Mustafa Magu, ya bukaci a saka darasin yaki da cin hanci da rashawa cikin kundin karatun makarantu a Najeriya, yana mai jaddada cewa dole ne kowa ya taka rawa domin cimma nasara a wannan yaki.
Magu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin karrama shi a matsayin mamba na musamman na Cibiyar ƙwararrun masana Forensik da binciken Zamba ta Najeriya (CIFCFIN), da aka gudanar a cibiyar nazarin dokokin Majalisa da Dimokuradiyya (NILDS), Abuja.
Ya bayyana cewa babu wani mutum guda ko kuma hukuma da za ta iya lashe wannan yaki ita kaɗai, yana mai cewa dole ne a tashi baki ɗaya a matsayin al’umma domin magance matsalar cin hanci.
Ya bukaci CIFCFIN ta yi aiki tare da kotuna, makarantu da ƙungiyoyin ƙwararru wajen ƙarfafa amfani da shaidar forensik a kotu da kuma shigar da darasin yaki da cin hanci a makarantu tun daga matakin firamare har zuwa sakandare.
Magu ya kuma tunatar da kalubalen da suka fuskanta wajen kafa hukumar kula da bayanan kuɗi ta ƙasa (NFIU), da kuma yadda aka yi rashin fahimta a farko game da dokokin wanke kuɗi, yana mai cewa wayar da kan jama’a abu ne da ya zama dole a ci gaba da yi.
Da yake magana da manema labarai bayan bikin, Magu ya nuna farin cikin sa bisa wannan karramawa, yana mai cewa hakan na ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da aikin yaki da rashawa.
Ya ce binciken forensik muhimmin ginshiƙi ne wajen tabbatar da gaskiya a shari’o’in cin hanci.
A nasa jawabin, shugaban farko na CIFCFIN, Dakta Iliyasu Gashinbaki, ya yaba da rawar da Magu ya taka a EFCC duk da ƙalubale, yana mai cewa tarihin gaskiya kan nuna mutanen da suka tsaya tsayin daka wajen yaki da rashawa.
Ya ce shugabancin EFCC shi ne “aikin da ya fi wahala a Najeriya.”
Magu, wanda ya kasance daga cikin masu kafa EFCC tun 2003, ya jagoranci hukumar a matsayin shugaban rikon kwarya daga 2015, inda ya gudanar da muhimman bincike ciki har da dawo da kudaden Abacha, badakalar Halliburton da kuma zamba a tallafin man fetur.
Yanzu haka yana ci gaba da karatun digirin digirgir (PhD) a tsaro da dabarun mulki a Jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi.













































