UNGA80: Shettima ya gana da Guterres,tare da tattauna batun neman kujera a kwamitin tsarona MDD

IMG 20250926 WA0001 750x430

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya gana da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), António Guterres, a hedikwatar MDD da ke New York, inda suka tattauna batutuwa masu muhimmanci ciki har da burin Najeriya na samun kujerar dindindin a kwamitin tsaro na MDD.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ce taron ya gudana ne a gefen zaman babban taron MDD karo na 80 (UNGA80), inda Shettima ya gabatar da jawabin ƙasa a madadin shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Shettima ya jaddada bukatar ƙarin tallafin MDD ga Najeriya, yana mai cewa ƙasar na neman matsayi na dindindin a kwamitin tsaro.

Haka kuma, Shettima da Guterres sun tattauna batutuwan da suka shafi cimma manufofin ci gaba mai ɗorewa (SDGs), sauyin yanayi, da kuma haɗin gwiwa don ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya da nahiyar Afirka baki ɗaya.

Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa MDD na da ƙarfi a Najeriya, inda da dama daga cikin hukumominta ke aiki a ƙasar.

Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziƙin zamani Dakta Bosun Tijani, ya bayyana farin cikin Guterres kan yadda Najeriya ta ƙaddamar da babban tsarin harsuna da fasahar zamani (AI) a kwanakin baya – wanda shi ne na farko a nahiyar Afirka da gwamnati ta tallafa.

Karin labari: Mafita ta ƙasashe biyu ita ce hanyar samun zaman lafiya a Falasɗinu – Gwamnatin tarayya

Ya ce babban sakataren MDD ya nuna burin ganin Najeriya ta taimaka wa sauran ƙasashen Afirka wajen amfani da AI don ci gaban tattalin arziki da al’umma.

Haka nan, karamin Ministan harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Yusuf Sununu, ya ce Shettima ya yi bayani kan ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen magance matsalolin jinƙai da talauci.

Ya bayyana cewa ƙasar na da jerin sunayen jama’a mafi girma a nahiyar, wanda ya ƙunshi gidaje kusan miliyan 18.9, tare da sama da ‘yan ƙasa miliyan 8.1 da aka tallafa musu ta hanyar shirin biyan kuɗin jinƙai.

Sununu ya kara da cewa an tattauna matsalolin rage tallafin kuɗi daga hukumomin MDD, inda shirin tallafin abinci na duniya (WFP) ya riga ya taimaka wa sama da ‘yan Najeriya miliyan 1.3 da tallafin abinci na gaggawa.

A cewar shi, Guterres ya tabbatar wa Najeriya da ci gaba da goyon baya wajen ƙara ƙarfin ma’aikatar jinƙai, tabbatar da ingancin rijistar jama’a, da samar da ƙarin kuɗi domin ayyukan tallafi da rage talauci.

Babban sakataren MDD ya kuma yaba da tallafin da gwamnatin Najeriya ke bai wa ƙungiyar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da mara mata baya a burinta da fatanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here