Majalisar Wakilai ta sanar da taron jin ra’ayin jama’a kan wasu muhimman kudurori guda hudu na sake fasalin haraji.
Za a fara sauraron ra’ayin ne daga ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu zuwa Juma’a 28 ga Fabrairun 2025, a harabar majalisar dokokin kasa da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da kakakin majalisar, Rep. Akin Rotimi, Jr., ya fitar, za a gudanar da zaman ne a zauren taro mai lamba 028 da 231 a sabon ginin majalisar wakilai, wanda za a fara kowace rana da karfe 12:00 na rana.
Labari mai alaka: Ƙudirin haraji ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai
Taron dai zai hada manyan masu ruwa da tsaki, da suka hada da hukumomin gwamnati, da shugabannin ‘yan kasuwa, da masana harkokin haraji, da wakilai daga kamfanoni masu zaman kansu, da kungiyoyin farar hula.
Manufar ita ce a samar da ingantacciyar tattaunawa da tattara shawarwari don tabbatar da adalci da ingantaccen tsarin haraji a cikin ƙasa.
Majalisar Wakilai ta bukaci masu ruwa da tsaki da su taka rawar gani wajen ganin an gudanar da taron jin ra’ayin jama’a, tare da jaddada cewa sauye-sauyen da ake shirin yi na neman daidaita manufofin harajin Najeriya da ingantattun ayyuka na duniya tare da tallafawa ci gaban tattalin arziki da kwanciyar hankali yayi tasiri.