‘Yan sanda sun dakatar da aiwatar da binciken lasisin baƙin gilashin mota saboda umarnin kotu

tinted permit 716x430

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Laraba ta bayyana cewa ta dakatar da aiwatar da binciken lasisin baƙin gilashin mota bayan samun umarnin kotu da ta dakatar da wannan aiki.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya, Sp Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan yayin hira da ita a tashar talabijin ta AIT.

Ta ce rundunar ta dakatar da binciken ne bayan ta karɓi umarnin kotu na daina wannan aiki.

Adeh ta bayyana cewa wannan dakatarwa za ta ci gaba har sai an samu hukuncin kotu a kan shari’ar da ke gudana, inda ta jaddada cewa rundunar ba za ta sabawa doka ko kotu ba, kuma za ta jira sakamakon hukunci kafin ci gaba da aikin.

Karin labari: Rundunar ƴan sanda ta ce, har yanzu ba ta samu takardar umarnin kotu kan lasisin baƙin gilashin mota ba

Ta kuma yi bayani cewa manufar dokar hana sanya baƙin gilashin motar shi ne don tsaro, saboda an samu wasu laifuka da ake aikatawa ta amfani da motoci masu baƙin gilashin da ba a iya ganin cikin su.

A cewarta, rundunar ‘yan sanda ba ita ta kirkiro dokar ba, aiki kawai take yi na aiwatar da abin da doka ta tanada.

Ta ce manufar ba don tara kudi ba ce, domin duk kuɗaɗen da ake biya dangane da lasisin baƙin gilashi ana turawa kai tsaye cikin Asusun Gwamnatin Tarayya na (TSA), ba cikin asusun ‘yan sanda ba.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here