Kotun Kolin Najeriya ta ba da umarni ga lauyoyin da ke kula da shari’o’in daukaka kara da korafe-korafen da aka tsara za a saurara tsakanin watan Satumba zuwa Disamba 2026, da su loda dukkan takardun shari’ar da suka dace a dandalin yanar gizo na tsarin gudanar da kararrakin Najeriya (Nigerian Case Management System) https://www.supremecourt.gov.ng/
Wannan umarni na cikin wata sanarwa da kotun ta fitar ta shafinta na X a ranar Talata.
A cewar sanarwar da Babban Rijistaran Kotun Koli, Kabir Akanbi, ya sayya wa hannu ta bayyana, wannan umarni ya yi daidai da Sashe na 10(1) na Ka’idojin Gudanar da Shari’a na Kotun Koli na 2026.
Kotun koli lauyoyi shawarci lauyoyi da su duba jerin daukaka kara da bukatun shari’ar da aka tsara za a saurara ta hanyar ziyartar shafin yanar gizon Kotun, inda za su shiga sashen Litigation, su shiga Gudanar da Kararrakin Najeriya, sannan su sauke takardun da suka dace.
Sanarwar ta ce ana sa ran lauyoyi su duba jerin shari’o’in da aka tsara tsakanin watan Satumba zuwa Disamba kafin su loda dukkan takardun da suka shafi shari’o’insu.
“Bayan haka, ana bukatar Lauyoyi su loda dukkan takardun da suka shafi shari’o’insu, ciki har da “Record of Appeal”, “Briefs of Argument”, korafe-korafe da ke jiran hukunci da duk sauran takardun da aka shigar, kafin kwanaki 30 da ranar da aka kayyade don sauraron shari’ar, kamar yadda aka gindaya a Sashe na 10(1) na ka’idojin gudanar da shari’a na Babbar Kotun 2026 ya tanada,” in ji sanarwar.
Kotun ta bayyana cewa wannan bukata ta shafi duk shari’o’in daukaka kara da korafe-korafe da aka tsara za a saurara a cikin watanni hudu.
Ta roki lauyoyi su tabbatar sun bi wannan umarni domin saukake aiwatar da tsarin gudanar da shari’o’i ta hanyar yanar gizo.
“Kotun tana kira ga dukkan Lauyoyi su bi wannan doka da kyau domin saukake gudanar da “Nigerian Case Management System” cikin sauki da tabbatar da saurin kammala shari’o’i,” in ji Akanbi.












































