Wani dan Najeriya mai tsara shafukan yanar gizo, Aminu Kurami, ya kaddamar da shafin yanar gizo da aka kebe don tunawa da marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana wannan a matsayin kokarisa na kashin kai domin adana tarihin tsohon shugaban domin al’ummomi masu zuwa.
Kurami ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), inda ya ce ya samar da shafin ya samo asali daga sha’awar sa na kirkirar wani dandalin adana bayanai game da rayuwar Buhari, jagorancinsa da ayyukan sa na hidimar kasa.
A cewarsa, duk da cewa bas hi da wata dangantaka da tsohon shugaban, amma yana matukar girmama shi saboda jajircewarsa wajen yi wa kasa hidima, kuma ya yi imanin cewa gudunmawar shugabannin Najeriya ya kamata a rubuta su a tarihin kasa.
“Wannan shafin na yanar gizo yabo da girmamawa ne ga rayuwar Shugaba Buhari da abin da ya bari. An tsara shi ne domin ya zama sahihin dandamali da ‘yan Najeriya, dalibai, masu gudanar da bincike da al’ummomi masu zuwa za su iya samun bayani cikin sauki game da hidimar da ya yi wa kasa,” in ji shi.
Kurami ya bayyana cewa shafin yanar gizon na kunshe da tarihin rayuwar Buhari, tafiyar ta shugabanci, manyan nasarorinsa, jawabi, hotuna da kuma muhimman abubuwan da suka faru a lokacin da yake mulki.
Ya ce aikin ya dauki watanni masu yawa kafin a kammala, inda aka yi bincike sosai, tsare-tsare, samar da bayanai da kuma kirkirar shafin yanar gizon kafin a wallafa shi.
Injiniyan ya kara da cewa ya dogara ne da bayanai daga hukuma, manyan kafafen yada labarai ingantattu, bayanan tarihi, littattafai da sauran amintattun littattafan bincike domin tabbatar da gaskiyar bayanan da ke shafin.
A cewarsa, bangaren da ya fi wahala a cikin aikin shi ne tsara ayyukan shekaru da dama da Buhari ya yi a mulkin soja da kuma na demokradiyya domiya zama tarihin mai inganci dake da saukin fahimta.
Kurami ya lura da cewa Shugaba Buhari ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya, inda ya yi aiki a matsayin Shugaban Mulkin Soja da na demokradiyya da aka zaba shi.
Ya yi fatan cewa shafin yanar gizon zai taimaka wajen kiyaye wa da adana tarihin Najeriya ta hanyar samar da ingantaccen dandalin bincike na yanar gizo ga duk wanda ke sha’awar sani game da rayuwar marigayi shugaban da gudummawar sa.










































