Kungiyar SERAP mai rajin tabbatar da adalci a ayyukan gwamnati ta bukaci Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio, cewa ka da ya amince da shirin ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, na ginawa mataimakin shugaban kasa katafaren gida.
Bukatar hakan na zuwa ne ta cikin wata wasika da kungiyar ta fitar dauke da sa hannu mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP Kolawole Oluwadare.
Ta cikin wasikar mai kwanan watan 2 ga Disambar 2023, SERAP ta bukaci Akpabio da ya yi amfani da ikon dake hannun sa wanda kundin tsarin mulkin kasa ya bashi domin dakatar da shirin ministan Abuja na kashe naira biliyan 2 da miliyan 800 wajen gina wa mataimakin shugaban kasa katafaren gida.













































