Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta Kama banban mataimaki na musamman ga mai girma gwamnan Kano kan harkokin jami’an gwamnati Tasiu Al’Amin Roba, da kuma wani mai suna Abdulkadir Muhammad.
Kamen nasu na zuwa ne bisa zargin su da karkatar da kayan tallafin rage radadi da gwamnatin Kano ta bayar.
Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kano Muhammad Hussain Gumel ne ya tabbatar da kamen a zantawarsa da kamfanin dillancin Labarai NAN da safiyar ranar Lahadi.
A cewar kwamishinan sun sami rahoton cewa wadanda ake zargin suna sauya buhun kayan tallafin zuwa na sayarwa, kuma jami’an su sun kama su ne a ma’ajiyarsu dake Sharada da buhuna 200 wadanda babu komai a ciki.
Yace da zarar sun kammala gudanar da bincike za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin daukar matakin da ya dace.
Ko a ranar asabar ma sai da gwamnatin Kano ta bankado wani wajen ajiyar kayan tallafin da ake karkatar da su zuwa na sayarwa.
Sakataren yada labaran gwamnatin Kano Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema Labarai.













































