Hukumar kula da gidajen Yari ta musanta zargin fitar da Emefiele daga gidan Gyaran hali  

Godwin Emefiele 750x430
Godwin Emefiele 750x430

Kwanturola Janar na hukumar kula da gidajen Yari ta Kasa, Haliru Nababa, ya musanta zargin fitar da Godwin Emefiele, da karfi daga hannunta.

A cewarsa Hukumar DSS da Hukumar EFCC ba su yi yunkurin haka ba.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai kan kararrakin jama’a, biyo bayan koken da cibiyar tabbatar da adalci ta gabatar.

Sai dai dan majalisa Mike Etaba, shugaban kwamitin ya yi watsi da koken cibiyar.

Karanta Wannan:Jami’an DSS sun kubutar da Mahaifiyar Dan Takarar Sanatan Jigawa ta Tsakiya daga Hannun Yan bindiga

Sylvanus Tahir (SAN), Daraktan Sashen Shari’a da Laifuka na EFCC, ya ce bai dace a shigar da karar ba saboda yana da alaka da wata shari’ar da ta shafi kotu.

Nababa, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar Konturola Janar mai kula da ayyuka Nwakeze Emmanuel, ya ce irin wannan yunkurin ba abu ne mai sauki ba.

Wakilin lauyoyin na EFCC, Tahir, ya ce tun da farko, “Koken da muka yi la’akari da shi kan wata shari’ar da ke gaban kotu ce’’.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here