Yan sandan farin kaya sun kubutar da Hajiya Binta Ibrahim, mahaifiyar tsohon Dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Kiyawa da Dutse a zauren Majalisar tarayya kuma Dan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya Honorable Tijjani Ibrahim Gaya daga hannun masu garkuwa a Kano.
Jaridar Solacebase ta tattaro cewa Yan bindigar sun sace Hajiya Binta Ibrahim, ne da misalin karfe 9:10 pm na daren ranar Litinin 20 ga watan Yunin shekarar 2022, a gidanta dake Unguwar Tsangayawa Yamma a garin Kiyawa.
Mai magana da yawun Rundunar yan sandan jihar Jigawa Lawan Shisu Adamu, ne ya tabbatar da kubutar da Hajiya Binta Ibrahim, sai dai bai yi wani karin bayani ba.
Shisu ya ce, an ceto Hajiya Bintan ne a rukunin gidajen Danladi Nasidi da ke Karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.
Wasu majiyoyi daga danginsu sun shaida cewar tun da farko wadanda suka sace Hajiya Binta sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 kafin daga bisani jami’an tsaro na farin kaya DSS su ceto ta.
Da aka tuntubi hukumar ta DSS ta ki cewa komai kan lamarin, sai dai wani jami’in hukumar ya tabbatar da aikin da kuma ceto Mahaifiyar Dan takarar Sanatan.
A cewar majiyar tsaron, jami’an tsaro na farin kaya DSS sun ceto Hajiya Binta da misalin karfe 4:00am na Asubahin ranar Asabar bayan sun kai hari a maboyar masu garkuwar.
Tuni dai aka ce tsohon Dan majalisar ya tarbi mahaifiyarsa cikin koshin lafiya kuma suna kan hanyarsu ta komawa gida Kiyawa.













































