Kungiyoyin NASU da SSANU sun tsawaita wa’adin yajin aikin da suke yi

SSANU NASU
SSANU NASU

Kungiyar ma’aikatan Jami’o’i ta kasa NASU da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya wato SSANU, sun tsawaita yajin aikin sa suke yi da watanni biyu.

Tsawaita wa’adin yana kunshe ne a wata takardar da aka raba wa shugabannin rassan kungiyoyin biyu, kuma aka rabawa manema labarai ranar Juma’a.

Sanarwar mai kwanan watan 21 ga watan Yunin shekarar 2022, ta samu sanya hannun babban sakataren kungiyar NASU, Prince Peters. A. Adeyemi, da kuma Mohammed N. Ibrahim.

Sanarwar ta bayyana wasu nasarorin da aka samu kan batutuwan da ake takaddama a kai, amma ta ce, duba da yadda har kawo yanzu gwamnati ta kasa warware matsalolin da ake takaddama a kai, yana da kyau a bada damar cika alkawuran gaba daya kafin a kai ga karshen yajin aikin.

Kazalika sanarwar ta kara da cewa kungiyoyin NASU da SSANU sun samu nasara kan biyan mafi karancin albashin ma’aikata, wanda tuni duk ma’aikatan suka amfana.

Sanarwar ta godewa ‘ya’yan kungiyar bisa yadda suka ci gaba da yajin aikin duk da kuwa hana su albashi da aka yi, baya ga barazana da tsangwama da suke fuskanta, inda ta ce a ci gaba da baiwa kungiyoyin goyon bayan da ake bukata domin cimma bukatunsu.

Ya bukace su da su ci gaba da rike madafun iko a sassan kungiyoyin, yana mai cewa “yayin da muke kara kusantar nasara a hankali tare da yin watsi da jita-jita da labaran karya kala-kala, musamman a shafukan sada zumunta, amma sun dogara ga shugabannin kasa don samun bayanai na gaskiya kan matsayin gwagwarmayar da ke gudana.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here