Ilimin Yara Mata: Sarkin Katsina ya yi barazanar soke shirin AGILE a fadin Jihar

Emir of Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman
Emir of Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir, ya bayyana aniyarsa ta dakatar da shirin AGILE daga jiharsa.

Alhaji Kabir ya ce shirin bai dace da tsarin addinin Musulunci da na al’adun yankin ba, don haka yana zubar da mutuncin iyaye da al’umma.

Sarkin ya bayyana haka ne a karshen mako a fadarsa, lokacin da ya nada wasu sabbin mukamai.

Karanta wannan:Tinubu ya bukaci Majalisar Dattijai, ta tabbatar da Kwamishinonin hukumar kidaya 19

Ya ce dole ne a daina aiwatar da shirin AGILE a jihar Katsina, kuma ba zai bari a yi katsalandan a harkar ilimi da ake da shi tuntuni ba.

Emir of Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman

Idan za a iya tunawa, wata kungiyar farar hula da ake kira da Kungiyar Matasan Kano, ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta kafa wani kwamitin bincike domin tantancewa tare da bankado wasu boyayyun akidu da ake zargin cewa suna cikin shirin na AGILE.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Shirin AGILE wani shiri ne da bankin duniya ke tallafawa domin inganta ilimin sakandare na ‘yan mata masu tasowa a Najeriya, wadanda ke tsakanin shekaru 10 zuwa 20.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here