Tinubu ya bukaci Majalisar Dattijai, ta tabbatar da Kwamishinonin hukumar kidaya 19

Senate
Senate

Majalisar dattawa ta sanar da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na neman a tabbatar da sunayen kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa NPC guda 19.

Wadanda aka nada sun hadar da:

  1. Emmanuel Eke (jihar Abia)
  2. Clifford Zirra (jihar Adamawa)
  3. Chidi Ezeoke (jihar Anambra)
  4. Isa Buratai (jihar Borno)
  5. Alex Ukam (jihar Cross River)
  6. Blessyn Brume-Ataguba (jihar Delta)
  7. Jeremiah Nwankwegu (jihar Ebonyi)
  8. Tony Aiyejina (jihar Edo)
  9. Ejike Ezeh (jihar Enugu)
  10. Abubakar Damburam (jihar Gombe)
  11. Uba Nnabue (jihar Imo)
  12. Dogon Garba (jihar Kaduna)
  13. Aminu Tsanyawa (jihar Kano)
  14. Yori Afolabi (jihar Kogi)
  15. Olakunle Sobukola (Jihar Ogun)
  16. Temitayo Oluwatuyi (jihar Ondo)
  17. Maryama Afan (Jihar Plateau)
  18. Ogiri Henry (Jihar Rivers)
  19. Sanay Sale (Jihar Taraba)

Karanta wannan:JAMB zata fara Jarrabawar auna fahimta ga masu neman shiga Jamia’a kai tsaye

Shugaban ya kuma nemi majalisar da ta tabbatar da nadin Bashir Indabawa a matsayin wanda zai kula da yankin Arewa masoYamma.

Sai Enorense Amadasu a matsayin wanda zai kula da Kudu maso Kudu da Babajide Fasina a matsayin wanda zai kula da Kudu maso Yamma.

Shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio ya gabatar da sunayen ga hukumar kula da tantancewa ta kasa (NIMC) domin ta bada rahoton cikin makonni biyu.

Senate 1 750x430
Majalisar Dattawa

Kazalika Majalisar Dattawa ta amince da nadin Desmond Akawor a matsayin kwamishinan da zai wakilci jihar Ribas a hukumar tattara kudaden shiga da kuma kasafin kudi (wato RMAFC).

Nadin ya biyo bayan rasuwar tsohon kwamishinan na RMAFC daga jihar Ribas, Asondu Temple.

Majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa ranar 20 ga watan Disamba domin ci gaba da tattaunawa kan kudirin kasafin kudin shekarar 2024.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here