Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta ce za a fara yi wa masu neman shiga jami’a daga aji biyu (wato DE) jarabawar auna fahimta daga shekarar 2024.
Magatakardan hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Wata sanarwa da Hukumar ta fitar a ranar Litinin tace daga shekarar 2024, JAMB za ta fara gudanar da jarrabawar cancanta ga duk wanda ya nemi shiga kai tsaye.
Karanta wannan: CAC ta ce za ta soke rijirtar kamfanoni dubu 91 da 843 sakamakon kin sabunta bayanan su na shekara da ita
Ya ce duk masu neman DE za su samar da wadannan abubuwan a lokacin yin rajista:
Lambar rajista ta makarantar da ya kammala da takaradar kammala karatun da shekarar kammala karatu da kuma takardar samun gurbin karatu.