CAC ta ce za ta soke rijirtar kamfanoni dubu 91 da 843 sakamakon kin sabunta bayanan su na shekara da ita

Corporate Affairs Commission CAC
Corporate Affairs Commission CAC

Hukumar kula da kamfanoni CAC ta ce za ta soke rijirtar sunayen kamfanoni dubu 91 da 843 sakamakon kin sabunta bayanan su na shekara da ita.

A cikin jerin sunayen da aka buga a shafinta Internet, hukumar ta zayyana kamfanoni dubu 91 da 843 da aka soke.

Wannan adadi ya kasa da wanda hukumar ta fitar a watan Agusta wanda ya kai dubu 94 da 581.

Karanta wannan:Gwamnatin Osun ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin sanya guba a abincin wasu daliban Firamare 18

Idan za a iya tunawa, a watan Yuli ne magatakardar hukumar Garba Abubakar, ya bayyana cewa hukumar za ta soke kamfanoni dubu 100 da suka yi rajista daga ma’adanar bayanan ta saboda sun kasa shigar da rahoton shekara-shekara.

Abubakar ya sanar da cewa hukumar za ta aike da sanarwar gargadi ga kamfanonin da abin ya shafa kafin fara wannan mataki kamar yadda yake a sashi na 692 na dokar CAMA ta 2020.

Sai dai sanarwar tace duk kamfani da ya sabunta bayanansa na shekara amma har yanzu sunansa na jerin sunayen, to su aika wasika tare da shaidar yin rajista zuwa compliance@cac.gov.ng.

Sannan ya bayyana cewa, haramun ne duk wani kamfani da aka cire sunansa daga rajistar kamfanoni ya ci gaba da kasuwanci har sai an kara mayar da sunansa cikin rajistar bisa umarnin babbar kotun tarayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here