Babu wani Maniyyaci da zai rasa aikin Hajjin 2025 saboda soke kwangilar da aka yi – Shugaban NAHCON

NAHCON Chairman Prof Abdullahi Saleh Usman sabo 750x430

Shugaban hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ya ce aikin Hajji na 2025 zai kasance ba tare da matsala ba.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ga wani labari da ke cewa “dubban maniyyatan Najeriya na iya kasa zuwa aikin Hajjin 2025 saboda soke kwangilar Masha’ir da shugaban hukumar Alhazai (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi.

Idan dai za a iya tunawa, kungiyar manyan jami’an hukumar jin dadin Alhazai ta jiha, hukumomi, sun koka kan yadda dubban maniyyatan Najeriya ba za su iya zuwa aikin Hajjin 2025 ba saboda shugaban (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya soke kwangilar Masha’ir.

Sakataren kungiyar kuma babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Adamawa, Abubakar Salihu, wanda ya yi magana a madadin kungiyar, ya yi wannan tsokaci ne a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi.

Taron ya kunshi manyan shuwagabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jiha, hukumomi, da kwamitocin Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Labari mai alaƙa: Dubban ‘yan Najeriya ka iya rasa zuwa aikin Hajjin 2025 yayin da NAHCON ta kawo karshen yarjejeniyarta da Saudiyya

Salihu ya ce matakin da shugaban NAHCON ya yi na soke kwangilar da aka rattabawa hannu da kamfanin samar kula da mahajjata na Saudiyya Mashariq AL-Dhahabiah na iya hana ‘yan Najeriya bizar aikin Hajjin 2025, tare da hana su zuwa aikin Hajji mai tsarki.

Sai dai Abdullahi Saleh ya yi watsi da labarin a matsayin karya, yana mai cewa babu wani mahajjaci da zai kasa zuwa aikin Hajjin 2025 domin hukumar ta dauki matakin ganin an aiwatar da aikin.

Ya ce labarin an yi shi ne domin a bata masa suna a matsayinsa na malamin addinin musulunci kuma kwararren mai gudanarwa.

Ya ce, “Hukumomin Saudiyya da kansu ne suka soke kwangilar kamfanonin biyu. An sake dawo da su kuma sun sake soke kwangilar.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa na yi gaggawar tafiya Saudiyya don ganawa da hukumomin da abin ya shafa. An shirya taro a jiya (Lahadi) amma bai samu ba saboda wasu dalilai kuma za a zauna yau.

Daily Trust

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here