Kotu a Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe maigidansa

Hanging rope 1

Babbar Kotun a jihar kano ta yanke wa Abdulaziz Adamu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan tabbatar da cewa ya kashe maigidan nasa, Alhaji Ali Alhassan, bayan garkuwa da shi tare da karɓar kudin fansa na naira Miliyan Goma Sha Biyar daga iyalinsa.

Rahoton ya bayyana cewa Adamu, mazaunin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, ya fuskanci tuhumar haɗin baki da aikata garkuwa da mutum da kuma kisan kai, yayin da wanda ake tuhuma na biyu, Abdullahi Alhassan daga unguwar Ɗanladi Nasidi, aka wanke shi daga laifin gaba ɗaya.

Binciken shari’ar ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Yuni na shekarar 2024 a yankin Dawaki Kudu, lokacin da Adamu ya haɗa kai da Abdullahi wajen sace Alhassan, sannan suka karɓi kudin fansa daga iyalinsa.

Bayan karɓar kudin fansa, laifin ya ci gaba da bayyana cewa wanda ake tuhuma ya bugi Alhassan a kai da kirji da manyan sanduna, lamarin da ya jawo mutuwarsa, daga nan kuma aka binne gawarsa a gidan Adamu da ke Dawaki Kudu ba tare da sanarwa ga hukumomi ba.

Shaidu biyu da aka gabatar a kotu da bayanin amincewar da aka danganta ga Adamu sun ƙarfafa tuhumar, duk da cewa ya musanta laifukan da ake zarginsa da aikatawa yayin zaman shari’ar da ya gudana.

A hukuncin da mai shari’a Aisha Mahmoud ta yanke, an tabbatar da cewa hujjojin da aka gabatar suna da isasshen ƙarfi wajen tabbatar da cewa Adamu ne ya aikata laifin kisan da ya jawo mutuwar Alhassan.

Kotun ta tabbatar da cewa sashe na 86, 87, 273, 221 sakin (a) na kundin hukunta laifuka na jihar Kano sun tabbatar da laifin da ke kan Adamu, yayin da aka wanke Abdullahi saboda rashin shaidar da ta gamsar da kotu da cewa yana da hannu a lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here