An shiga fargaba a birnin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a ranar Alhamis bayan rahoton cewa mataimakin gwamnan jihar, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya yanke jiki ya faɗi ƙasa kuma an garzaya da shi zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Yenagoa.
Lamarin ya faru ne kimanin ƙarfe 1:30 na rana a ofishinsa, lamarin da ya sa aka gudanar da ceton gaggawa domin kai shi sashen gaggawa na asibitin.
Shaidu sun bayyana cewa halin da yake ciki ya yi tsanani lokacin da aka isa da shi asibiti.
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa ana kula da lafiyarsa a sashen kulawa ta musamman na cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Yenagoa.
Sai dai ba a samu wata sanarwa ta hukuma ba game da abin da ya haifar da matsalar lafiyar, sai dai majiyoyi sun ce yana iya alaƙa da matsalar zuciya.
Majiyar da ke kusa da mataimakin gwamnan ta danganta lamarin da yawan ayyukansa na yau da kullum, tana mai cewa yana yawan aiki fiye da kima, ya kamata ya ba kansa lokaci ya huta.
Jami’an tsaro sun mamaye harabar asibitin, yayin da manyan jami’an gwamnati suka ziyarci wurin domin nuna damuwa.
Har zuwa yanzu ba a sami damar yin magana da mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Mista Doubara Atasi ba, amma majiyoyi daga asibitin sun tabbatar cewa ana ba Ewhrudjakpo kulawa mafi inganci kuma yana cikin yanayi mai kwanciyar hankali.












































