Hatsarin Mota ya halaka daliban Jami’ar Jos guda 8 

Accident 750x388 (1)

 Akalla dalibai takwas na jami’ar Jos sun rasu a wani mummunan hatsarin mota a kan titin Zariya da ke cikin gundumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

Jami’in wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haddura ta tarayya FRSC, reshen Filato, Mr Peter Longsan ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawar sa da manema labari.

Ya ce, hadarin ya faru da safiyar Alhamis da misalin ƙarfe 2:30 na dare, inda aka bayyana cewa hatsarin ya shafi motoci biyu, inda dalibai bakwai suka rasu nan take, yayin da ɗaya daga cikin sauran da suka jikkata ya rasu a asibiti, wanda hakan ya kai yawan waɗanda suka mutu zuwa takwas.

Peter, ya bayyana cewa gudun wuce Sa’a a kan hanya ne ya janyo aukuwar hatsarin, wanda ya rutsa da tirela da kuma wata ƙaramar bas wadda ke ɗauke da dalibai 11 na jami’ar Jos.

Ya tabbatar da cewa sauran mutum uku suna karɓar magani a asibiti, kuma dukkan waɗanda hatsarin ya rutsa da su maza ne gaba ɗaya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa ana hasashen cewa daliban na dawowa daga wani taron nishaɗi ne kafin hatsarin ya faru.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here