Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, bayan ta yi masa tambayoyi kan zargin yin almundahana da kudade.
Tambuwal, wanda kuma ya rike mukamin shugaban majalisar majalisar wakilai, ana zarginsa da zambar kudi kusan Naira biliyan 189 a lokacin da ya ke gwamna.
Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an saki Tambuwal ne bayan ya bayar da bayanan da masu binciken suka bukata.
Majiyar ta ce “An riga an ba shi beli bayan an samu duk wasu bayanai da hukumar ke bukata daga gare shi, kuma nan ba da jimawa ba zai bar shalkwatar mu bayan kammala cika sharuddan belinsa.”
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da faruwar lamarin a daren yau Talata, amma ya ki cewa komai.
Tambuwal ya amsa gayyatar EFCC ne a ranar Litinin, 12 ga watan Agustan shekerar nan da muke ciki ta 2025, inda ya isa shalkwatar hukumar da ke Abuja da karfe 11:16 na safe.













































