Mahaifiyar dan majalisar dokokin Kano da aka sace, Hajiya Zainab, ta samu ‘yanci bayan an biya ta kudin fansa.
An sace Hajiya Zainab, mahaifiyar Isiyaku Ali Danja, shugaban marasa rinjaye, majalisar dokokin jihar Kano a gidanta da ke karamar hukumar Gezawa a Kano, a ranar 12 ga Janairu, 2021.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase a ranar Talata, dan majalisar ya ce mahaifiyarsa ta samu ‘yanci bayan an biya N40m.
Ali Danja wanda shi ne kakakin majalisar ya ce suna kan hanyarsu ta dauko ta ne daga wata karamar hukuma da ke jihar Jigawa inda masu garkuwa da mutane suka ajiye ta.













































