Super Eagles sun dawo daga Kamaru

41E0ACD7 2F47 4A69 B907 1A40A847DCC9
41E0ACD7 2F47 4A69 B907 1A40A847DCC9

A yau Talata ne tawagar Super Eagles ta dawo Najeriya daga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2021 da ke gudana a kasar Kamaru.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa tawagar ‘yan wasan da jami’an ta sun dawo ne ta jirgin haya daga Garoua inda suka buga wasanni hudu.

Sun isa ne da karfe 1:10 na safe a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, inda jami’an hukumar kwallon kafar Najeriya NFF suka tarbe su.

Jami’an NFF sun samu jagorancin babban sakataren hakumar Mohammed Sanusi, tare da rakiyar mambobin kwamitin zartarwa da suka hada da Yusuf Ahmed da Shehu Dikko.

Da yawa daga cikin ‘yan wasa da jami’ai sun sauko daga jirgin, tare da sauran mutane wadanda suka hada da ‘yan kungiyoyin magoya baya da kuma jami’an yada labarai.

Daga bisani jirgin ya nufi Legas, inda ya sauke wasu daga cikin ‘yan wasa da jami’ai da suka rage, yayin da sauran suka nufi Transcorp Hilton inda nan ne masaukin su.

Muhammed Sanusi ya yi maraba da ‘yan wasan tare da yaba musu bisa kokarin da suke yi a kasar Kamaru, inda ya ce yanzu lokaci ya yi da za su sa ido a kan aikin samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022.

Daga baya kyaftin din kungiyar, Ahmed Musa, ya shaidawa NAN cewa basu ji dadin yadda kungiyar ta kasa cimma burinta a gasar AFCON ta 2021.

Zamu mayar da hankali kan wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da Ghana ta Black Stars a watan Maris.  Amma a yanzu zamu koma kungiyoyin da muke taka leda domin ci gaba da wasanni kafin zuwan lokacin wancan wasan.

Super Eagles, bayan da ta yi nasara sau uku a zagayen farko na gasar da ta samu tagomashi, ba ta samu damar  iya wucewa zagaye na biyu ba, bayan da suka sha kashi a hannun Tunisia ci 0-1.

Ana sa ran ‘yan wasan za su koma kungiyoyinsu na kasashen waje nan da kwana daya ko biyu masu zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here