Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya, da mataimakinsa Musa Bawa Musa Yankuzo, sun sha kaye a hannun ‘yan takarar adawa na jam’iyyar PDP dasuka fafata a ranar Asabar da ta gabata.
Jami’in tattara sakamakon zaben mazabar Zurmi ta Yamma, Ismail Mudassir Moriki, ya bayyana Bilyaminu Ismail na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar shugaban majalisar.
Ismail ya samu kuri’u 11,213 inda ya doke shugaban majalisar wanda ya samu kuri’u 9,530.
Hakazalika, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Yankuzo, ya sha kaye a zaben sa da ya sake tsayawa takara a karkashin jam’iyyar, inda Bello Muhammad Mazawaje, wanda ya samu kuri’u 21,197 a gaban Yankuzo da kuri’u 13,820.
A halin da ake ciki, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar na ranar Asabar, jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara, a ranar Litinin, ta zargi gwamna Bello Matawalle da yin garkuwa da jami’in tattara zabe na karamar hukumar Maradun na jihar.
A wata sanarwa da ofishin PDP ya fitar a Gusau, babban birnin jihar, jam’iyyar adawa ta hannun ofishin yada labarai na Dauda Lawal ta bayyana cewa gwamnan wanda jigo ne a jam’iyyar APC mai mulki, yana cigaba da matsa lamba wajen kawo cikas wajen tattara sakamakon zaben gwamna da kuma kokarin magudin zaben.
Lawal ne ke kan gaba a Matawalle a kananan hukumomi biyar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana ya zuwa yanzu.













































