Gwamnatin jihar Kano ta nuna damuwa kan yadda al’umma suka karya dokar zama a gida a lokacin duban tsaftar muhalli na karshen watan Janairu.
Kwamishinan Ma’aikatar muhalli da kula da sauyin yanayi Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala duban tsaftar muhallin na karshen wata yau Asabar da aka gudanar a sassan ƙwaryar birnin Kano.
Dakta Dahir Muhammad Hashim ya ce, a wata mai zuwa Ma’aikatar za ta kara baza jami’an tsaro, tare da rufe wasu hanyoyi don hana zirga-zirga a lokacin da ya kamata kowa ya zauna gida don gyara muhallin sa.
“Mun lura da yadda dirbobi daga wasu jihohi makwabta ke shigowa Kano a lokacin duban tsaftar muhalli, don haka ba za mu lamunci wannan mataki na su na karya mana doka ba, za mu tsaurara matakai tare da rufe hanyoyin shigowa cikin a wata mai zuwa” in ji Dakota Dahir.
Karin karatu: Yadda duban tsaftar muhalli na ranar Juma’a ya kasance
“Sannan za su sake baza jami’an tsaro domin daukan matakin doka a kan masu kai kawo a lokacin duban tsaftar muhalli”.
Dakta Dahir Muhammad Hashim ya kuma nuna takaicin sa kan yadda wasu tashoshin mota suka karya doka ta hanyar ci gaba da ayyukan su na yau da kullum a lokacin duban tsaftar muhalli.
Kwamishinan ya yabawa mazauna unguwar Kauyen Alu da ke karamar hukumar Tarauni bisa kokarin da suke yi na tsaftace muhalli da suka hada da makabarta, magudanar ruwa, da kewaye.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmad Muhammad, ya yabawa kwamishinan bisa jajircewar sa wajen tsaftace muhalli.
Ya kuma ba shi tabbacin ci gaba da kokarin karamar hukumar na kawar da bahaya a fili da kuma inganta tsaftar muhalli.
A yayin zagayen, kotun tafi da gidanka mai kula da tsaftar muhalli ta kama wasu mutane 28 da suka karya doka, kuma jimillar kudin tarar da masu karya dokar suka biya ya kai naira dubu ₦78,000.













































