Daga Asabar ɗin nan 1 ga watan Fabrairu ne rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta fara aiwatar da tsarin inshorar kamfanoni na 3 a fadin kasar nan.
Aiwatar da dokar daidai ne da umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasa (IGP), Kayode Egbetokun.
IGP ya ce shirin na da nufin karfafa matakan kiyaye hanyoyin da kuma tabbatar da cewa duk masu ababen hawa sun bi ka’idojin inshora da aka gindaya don kare kansu da sauran mutane a kan hanyar.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Juma’a, ta ce: “A bisa umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sake nanata aiwatar da dokar da ta tilasta a rukuni na uku yin Inshora wanda zai fara ranar 1 ga Fabrairu, 2025.
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargadi masu ababen hawa kan rashin bin wannan muhimmiyar doka. Inda ta ce rashin mallakar ingantacciyar Inshora ta ɓangare na uku zai haifar da fuskantar tsauraran mataki, gami da tara ko duka biyun”.
“Daga ranar 1 ga watan Fabrairu, duk masu abin hawa a fadin kasar nan ana bukatar su mallaki inshora ta Uku yayin da suke tafiya, kuma wadanda ba su da inshorar ana shawarce su da a gaggauta mallaka don gujewa duk wani fushin hukuma”.
“Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya umurci dukkan kwamishinonin ‘yan sanda na jihohi da su tabbatar da aiwatar da dokar, domin jami’an ‘yan sanda za a ba su ikon gudanar da bincike tare da aiwatar da hukunci kan rashin bin ka’idojin da suka dace.