Gwamnan jihar Kwara, Mallam Abdulrahman Abdulrasaq ya ziyarci sabon Balogun Alanamu (Hakimin Gundumar Alamanu), Dakta Usman Abubakar Jos.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Dakta Usman Abubakar Jos, ya kasance babban Malami a sashin koyar da ilimin Lissafi na Jami’ar Ilorin, kuma shi ne Hakimi na 12 da mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, ya nada tun a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2022.
An dai shirya gudanar da bikin nadin sarautar sabon Hakimin ne a ranar 6 ga watan Mayun 2022,a Fadar Mai Martaba Sarkin Ilorin.
Nadin nasa ya biyo bayan rasuwar Mahaifinsa, kuma Bologun Alamanu na 11 Alhaji Abubakar Jos, wanda ya rasu a ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2021, yana da shekaru 97 a duniya.
Balogun Alanamu Hakimin Alamanu guda ne cikin ‘Yan majalisar Sarki kuma masu nada Sarkin Masarautar Ilorin.
Gwamnan ya kuma taya sabon Hakimin murnar nada shi a matsayin Bologun Alamanu, tare da bukatar shi da yin duk mai yiwu wa wajen gudanar da ayyukansa cikin adalci kamar dai Mahaifinsa.
A nasa bangaren sabon Hakimin (Balogun), Dakta Usman Jos, ya bawa Gwamnan tabbacin cewa zai taimakawa al’ummar Alamanu tare da nemo musu ayyukan ci gaba daga wajen hukumomi ta yadda ya dace.
Ya kuma yaba da goyon bayan da Gwamnan yake bawa Iyalai da kuma kafatanin al’ummar Alamanu, tsawon lokaci.













































