Rushewar wani bangare na sabon ginin harabar Majalisar Dokokin Jihar Gombe da ake ginawa ya yi sanadiyyar mutuwar ma’aikaci 1 tare da jikkata wasu mutum 7.
Mallam Danladi Adamu, Babban Sakatare a Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Gombe ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a cikin wata sanarwa da ya fitar a Gombe ranar Juma’a.
Adamu, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya ce ya faru ne da safiyar Juma’a kuma ya shafi wani bangare na rufin kofar shiga ginin da ake yi.
“Lamarin ya shafi ma’aikata 8 inda 7 suka samu raunuka kuma nan take aka kai su asibiti don samun kulawar likita.
“Biyar suna karbar magani a Asibitin Kwararru na Jihar Gombe, yayin da sauran biyu ke karbar magani a Asibitin Koyarwa na Tarayya, Gombe.”
Danladi ya kara da cewa an sanar da Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya faruwar lamarin kuma ya mika ta’aziyya ga iyalin mamacin.
Ya ce gwamnan ya ba da umarnin cewa a ba dukkan ma’aikatan da suka jikkata cikakkiyar kulawar likita da sue bukata gwamnati za ta dauki nauyi.
Sakataren ya ce gwamnan ya kuma ba da umarnin Ma’aikatarsa, tare da sauran hukumomin agajin gaggawa, masu tsari da na fasaha da suka dace, da su fara aikin tabbatar da tsaro da kuma gano abin da ya faru nan take.
Ya ce Yahaya ya kara ba da umarnin cewa mai aikin da kuma mai ba da shawara kan aikin su mika rahoton faruwar lamarin na hukuma (FIR) cikin sa’o’i 24











































