Babban Bankin Kasa na (CBN) ya bayyana cewa tsohuwar takardar naira 100 tana nan matsayin halaccen kudi, tare da yin gargadin cewa duk wanda ko kasuwanci da ya ki karbar takardar zai fuskanci hukunci bisa doka.
Wannan bayani ya biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu ‘yan kasuwa, kamfanoni da jama’a sun ki karbar tsohuwar takardar naira 100 saboda fargabar cewa sabuwar takardar bikin cikar Najeriya shekara 100 ta maye gurbata ta.
A cikin wata sanarwa da Mukaddashiyar Daraktan Sadarwa ta Banki, Hakama Sidi Ali ta sanya wa hannu, babban bankin ya ce duka takardar naira 100 ta tunawa da kuma tsohiwar har yanzu na nan a matsayin halaccen kudi kuma dole ne a karbe su a dukkan ma’amaloli a fadin kasar.
CBN ta bayyana cewa an fitar da takardar naira 100 ta tunawa ne don bikin cikar Najeriya shekaru 100, kuma ba a fitar da ita ba domin maye gurbin takardar naira 100 ta yau da kullum ba.
Ta yi gargadin cewa kin karbar takardar naira 100 ya sabawa tanadin dokar CBN kuma hakan zai iya rage wa mutane kwarin gwiwa a kan kudin kasa.
“Bankin ba zai yi jinkirin daukar matakan gaggawa na doka da suka dace kan duk wani mutum ko cibiya da aka samu ta saba ba,” in ji sanarwar.
Babban bankin ya sake jaddada aniyarsa na kare martabar Naira, kiyaye amincewar jama’a kan dukkan takardun kudi da ya fitar bisa ka’ida da kuma tabbatar da samun saukin yaduwar kudi a fadin kasar.
Ya roki ‘yan Najeriya da su karbi dukkan takardun kudi da CBN ta fitar bisa doka, kuma ta ba da shawarar ga jama’a masu bukatar karin bayani da su tuntubi Bankin ta hanyar hanyoyin sadarwarsa na hukuma.














































