Gwamnatin Kano ta tallafawa mahauta 1,900, za ta kafa masana’antu na zamani

IMG 20260717 WA0048 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba kayan tallafi ga mahauta 1,900 a ranar Alhamis ya raba kayan tallafi ga mahauta 1,900 a ranar Alhamis karkashin hukumar kasuwancin gida da tallace-Tallacen kan titi.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kammala shirye-shiryen kafa masana’antu na gida da na kasuwanci ga mahauta a wurare masu muhimmanci a fadin jihar a yayin taron.

Ya ce gwamnati ta riga ta sanya shirin na kafa wadannan cibiyoyi a cikin kasafin kudi na 2026, inda ya kara da cewa an kammala aikin sharar fage kuma za a fara aiwatarwa nan ba da dadewa ba.

A cewarsa, masana’antun za su hada da wurare na musamman ga mahauta, harkokin sarrafa nama, sarrafa fata da kuma cibiyar kula da fatarsana’ar fata, domin hadin gwiwa da zai yi amfani da dukkan kayayyakin dabbobi wajen samun riba da tattalin arziki.

“Wannan gwamnati ta riga ta sanya tanadi a cikin kasafin kudi na 2026 da aka amince da shi na kafa masana’antu na gida da na kasuwanci a wurare masu muhimmanci a jihar.

“Saboda haka, ina so in sanar da ku cewa an kammala aikin sharar fage kuma za a fara aiwatarwa nan ba da dadewa ba.”

A cewarsa, wadannan cibiyoyin sun yi daidai da manufofin Shugaba Bola Tinubu na inganta kayayyakin da aka samar a Najeriya.

“An kuma tsara su don su zama cibiyoyin samar da kayayyaki, kirkire-kirkire, da masana’antar fata.

Gwamnan ya ce wannan tallafi wani gagarumin ci gaba ne a cikin kudurin wannan gwamnati na ginawa da karfafa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here