Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur daga Naira 890 zuwa Naira 825 kowace lita, inda sabon farashin zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025.
A cewar kamfanin, rage farashin na da nufin saukaka wa ‘yan Najeriya matsalolin kudi, musamman gabanin azumin watan Ramadan, tare da marawa shirin farfado da tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.
Wannan shine karo na biyu da aka samu raguwar farashin man fetur a watan Fabrairun 2025, biyo bayan rage Naira 60 a farkon watan.
Karanta: Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa Naira 890 a kowace lita
A watan Disambar 2024, a lokacin bikin Kirsimeti, matatar Dangote ta kuma rage farashin man fetur da N70.50, inda ta rage farashin man daga N970 zuwa N899.50 kowace lita domin samar da sauki a lokacin bukukuwa.
A yanzu haka dai sabon gyare-gyaren, man Dangote zai kasance a kan farashi zuwa kasuwannin abokan hulɗa:
MRS Holdings Tashoshi:
Legas: N860 kowace lita
Kudu-maso-Yamma: Naira 870 kan kowace lita
Arewa: N880 kowace lita
Kudu-Maso-Kudu/Kudu-Maso-Gabas: N890 kowace lita
AP (Ardova Petroleum) & Heyden Station:
Legas: N865 kowace lita
Kudu-maso-Yamma: N875 kowace lita
Arewa: N885 kowace lita
Kudu-Kudu/Kudu-Maso-Gabas: N895 kowace lita
Matatar dangote ta baiwa al’umma tabbacin ci gaba da samar da albarkatun man fetur, tare da isassun tanadin da zai biya bukatun cikin gida da kuma rarar da ake samu na fitar da su zuwa kasashen waje, wanda hakan ke taimakawa wajen samun kudaden waje.
Kamfanin ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su tallafa wa wannan shiri, domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ci gajiyar rage farashin kai tsaye.