Rundunar sojin saman Najeriya ta ce za ta fara gudanar da cikakken bincike kan yadda aka yi ruwan wuta a wasu kauyuka biyu a Sokoto ranar Laraba.
A cewar mazauna yankin, lamarin da ya faru da misalin karfe 7 na safe a unguwar Gidan Sama da Rumtuwa da ke karamar hukumar Silame, ya yi sanadin mutuwar fararen hula 10 tare da jikkata wasu da dama.
An kuma bayyana cewa an kashe dabbobi, inda mazauna yankin suka ce wasu daga cikin gidajensu sun lalace sakamakon harin da jiragen suka kai musu.