Kashe-kashen Filato: Sojoji sun kama mutane 20 da ake zargi

nigerian army training
nigerian army training

Rundunar Operation Safe Haven (OPSH), ta kama mutane 20 da ake zargi da hannu a kashe-kashen da aka yi a yankin Tingbwa Gidan Ado da ke karamar hukumar Riyom (LGA) a jihar Filato.

Maj.-Gen. Abdulsalam Abubakar, Kwamandan OPSH ne ya bayyana hakan a wajen liyafar cin abincin Kirsimeti da aka shirya wa sojojin OPSH da shiyya ta 3 na sojojin Najeriya, ranar Alhamis a Jos.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, a ranar 22 ga watan Disamba, wasu ‘yan bindiga sun kai wa al’umma hari tare da kashe mutane 15.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here