Dalilin da ya sa Atiku ba zai iya zama shugaban kasa a 2027 ba

Dr. Doyin Okupe

 

Tsohon kakakin yakin neman zaben Peter Obi, Dr. Doyin Okupe, ya bayyana cewa bai dace Alhaji Atiku Abubakar ya tsaya takara a 2027 ba, duba da bukatar ci gaba da mulkin kudu.

A cewarsa, bayan da arewa ta yi shekaru takwas a mulki kafin zuwan Shugaba Bola Tinubu, ya kamata kudu ta kammala wa’adinta.

Ya kara da cewa duk da cewa Atiku na da cancanta sosai, amma siyasar yanki ba za ta ba shi damar nasara ba.

Okupe ya kuma ce tsohon dan takarar Labour Party, Peter Obi, na da karfi amma zai fuskanci kalubale wajen kayar da Tinubu, duba da irin nasarorin da yake samu yanzu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here