Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta kori Lauyan Jiha Mustapha Nura-Muhammad kan zargin kirkirar takardu, cin zarafin mukami, da rashin da’a a aiki.
Hakan na cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai ga Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Dr. Abubakar Tijjani-Ibrahim, ya fitar a Kano.
Sanarwar ta ce Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano ta amince da korar a ranar 1 ga Afrilu, biyo bayan shawarwarin Kwamitin Manyan Ma’aikata da ladabtarwa na Ma’aikata.
“Bincike ya nuna cewa lauyan, wanda aka dauka aiki a shekarar 2024, ya kirkiri sunaye da sa hannun manyan jami’an shari’a domin bayar da shawara ta shari’a mara izini da rudani a shari’o’in laifuka da ke gaban kotu.
“Ɗaya daga cikin shari’o’in, Kwamishinan ‘Yan Sanda da Umar Abubakar, wanda ke gaban kotun majistiri dake Gyadi-Gyadi, kan zargin fashi da makami.
“Bincike ya nuna cewa jami’in ya kirkiri suna da sa hannun F.T. Ahmad domin bayar da shawara ta shari’a da nufin hada wani da ba shi da alaka da lamarin, lamarin da ya kai ga kama mutumin da tsare shi,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa a wata shari’ar kuma, ta Gwamnati da Tukur Lawan da wasu mutum biyu, wadda ta shafi fashi da makami da garkuwa da mutane, lauyan ya kirkiri suna da sa hannun B.A. Ahmad, Babban Lauyan Jiha, domin dakatar da shari’ar ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar ta ce wanda ake zargi a wannan shari’ar, wanda a baya yana tsare, daga baya aka sake kama shi.
Ta bayyana cewa: “Ma’aikatar ta kafa kwamitin ladabtarwa na cikin gida domin binciken lamarin kuma ta bai wa jami’in damar kare kansa bisa ka’idojin ma’aikatar gwamnati.
“An tambayi jami’in sannan daga baya aka dakatar da shi har sai an kammala ladabtarwa.
“Daga baya aka mika lamarin ga Kwamitin Manyan Ma’aikata, Karin Matsayi da Ladabtarwa na Ma’aikata, wanda ya ba da shawarar a kore shi sabod rashin da’a karkashin Sashi na 4, Dokar 04406 na Dokokin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano.
“Wannan mataki ya yi daidai da kudurin gwamnatin Gwamna Abba Kabir-Yusuf na karfafa lissafi, ladabtarwa, gaskiya, da kwarin gwiwa a harkokin gwamnati da sashen shari’a.”
Da yake martani kan lamarin, Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru-Maude, SAN, ya ce ma’aikatar ba za ta lamunci ayyukan da ke raunana mutuncin tsarin shari’a ba.
“Masanan shari’a, musamman wadanda aka dora musu alhakin jama’a, dole ne su rike mafi girman matakin dabi’a, gaskiya, da kwarewa.
“Wannan gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen tsaftace sashen shari’a da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci cikakken sakamakon doka.
“Ma’aikatar ta fara shirin mika lamarin ga Kwamitin Ladabtarwa na Masana Shari’a (LPDC) domin daukar matakin sana’a, kuma za ta kuma bi hanyar shari’a ta laifi,” in ji shi. (NAN)












































