Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Mohammed Lawal Uwais, ya rasu ya na da shekaru 89 a duniya.
Uwais, wanda ya yi shekara 11 daga 1995 zuwa 2006 a matsayin alkalin alkalai, ya rasu ne a Abuja yau Juma’a, kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta shaida wa SolaceBase.
Majiyar ta ce, ana shirye-shiryen gudanar da sallar jana’iza da kuma binne shi.
Babban masanin shari’ar na Najeriya da aka haife shi a ranar 12 ga watan Yuni, a shekarar 1936, ya jagoranci kwamitin gyaran dokokin zabe da marigayi shugaba Umar Yar adua ya kafa wanda ya gabatar da shawarar yin garambawul a tsarin zaben Najeriya a 2008.













































